Putin: Abin da ya sa muke kai hari a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Putin ya ce yana so ya daidaita gwamnatin Assad.

Shugaban Russia, Vladimir Putin ya kare hare-haren da kasarsa ke kai wa a Syria, yana mai cewa tana yin hakan ne domin "kawo daidaito a halastacciyar gwamnatin Bashar al-Assad".

Mr Putin ya shaida wa gidan talabijin Russia da ke Moscow cewa yana so ya samar da yanayin da " 'yan siyasar kasar Syria za su yi ban-gishiri-in-baka-manda".

Ya musanta cewa Russia tana kai wa 'yan hamayya hare-hare, ba wai kungiyar IS ba.

Rahotanni na cewa dakarun Syria sun samu gagarumar nasara a yunkurin da suke yi na kawar da 'yan tawaye.

Turai na yin taro kan Russia

Rahotannin sun ce dakarun sun kwato garuruwan Idlib, Hama da kuma lardin Latakia a ranar Lahadi.

A ranar Litinin ne dai ministocin kasashen waje na Tarayyar Turai ke yin taro a Luxembourg domin tattauna wa kan hare-haren da Russia ke kai wa a Syria.