Madugun 'yan tawayen Sudan ta Kudu ya yi barazana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan tawaye a Sudan ta Kudu

Wani madugun 'yan tawaye a Sudan ta Kudu ya ce da wuya yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanyawa hannu makonni shida da suka gabata ta yi aiki -- kuma mai yiwuwa ya sake daukar makami.

Janar Johnson Oloni ya shaida wa BBC cewa gwamnati na yi wa yarjejeniyar makarkashiya ta hanyar kai wa fararen hula hari da kuma shirin sake shata iyakokin kasar wanda ya bayyana a matsayin kwace mulki.

Ya kara da cewa batun rabon filaye ne ya sanya kabilarsa ta dauki makamai, yana mai cewa ba za su ji kunyar komawa fagen daga ba.

A shekaru biyun da suka gabata, yakin basasa a Sudan ta Kudu ya yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a sannan miliyoyin mutane sun rasa muhallansu.