Amurka ta bai wa 'yan tawaye makamai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rikicin Syria ya kara rincabewa

Jirgin saman dakwan kaya na Amurka ya jefa sama da kunshi dari na kayayyaki da suka hada da albarusai da gurneti gurneti da makaman roka ga 'yan tawayen Syria da ke fada da kungiyar IS.

Jami'an ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce jiragen saman na C-17 wadanda jiragen yaki suka yi wa rakiya sun jefa kayayyakin tan hamsin da biyar a lardin Hasakah da ke arewacin Syria.

Amurka ta amince da shugabannin kungiyar kuma za su samu goyan bayan dakarun hadin guiwar da ke kasar.

A waje daya kuma Rasha ta ce jiragen yakinta sun kai hari a kan sama da wurare hamsin na kungiyar IS, wadanda suka hada da wuraran bincike da sansanonin samun horo da ma'ajin makamansu a larduna da dama na kasar ta Syria.

Ministocin harkokin waje na tarayyar Turai sun yi kira ga Rasha da ta dakatar da hare-haren da take kai wa ta sama a Syria nan take.

Ministocin sun tattauna kan batun a wajan taron da suka yi a Lexumbourg.