Sojojin Uganda za su fice daga Sudan ta Kudu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A watan Agosta ne shugabannin kasashen Uganda da Sudan ta kudu suka sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya.

Shugaban rundunar sojin kasar Uganda ya bayyana cewa, dakarun kasar za su soma fice wa daga Sudan ta Kudu a karshen wannan makon.

Hakan na daga cikin yarjejeniyar zaman lafiyar da kasashen biyu suka sanya hannu a watan Agusta, inda aka amince cewa dakarun za su janye kafin ranar 10 ga watan Oktoba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da wani madugun 'yan tawaye a Sudan ta Kudu, ya ce da wuya yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sanyawa hannu makonni shida da suka gabata ta yi aiki -- kuma mai yiwuwa ya sake daukar makami.

Dubban mutane ne suka rasa rayukan su tun da aka soma yakin basasa a kasar shekarar 2013.

Uganda ba ta bayyana ko dakarunta nawa ne ke cikin kasar, domin bai wa gwamnatin Sudan ta Kudu goyon baya.