Kamfanonin Barasa sun hada gwiwa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kamfanonin SABMiller da AB InBev suna shirin hada gwiwa.

Manyan kamfanoni barasa biyu na shirin hada gwiwa bayan da daya daga cikin su watau kamfanin SABMiller, ya amince abokin adawarsa Anheuser-Bush InBev ya mallake shi.

SABMiller ya ce ya yarda da tsarin mallake shi a farashin £44 a kan kowanne hannun jari bayan yunkurin da AB InBev ya yi har sau hudu domin ya mallake shi.

Cikin ire-iren barasar da AB InBev ke hadawa, sun hada da Budweiser da Stella Artois da Corona, shi kuma SABMiller na hada Peroni da Grotsch.

Idan aka cimma burin yarjejeniyar, wacce farashinta zai kai fan biliyan £70, sabon kamfanin da za a fitar zai rika hada kaso 30 cikin 100 na barasar duniya baki daya.

SABMiller yana daukan ma'aikata kusan 70,000 daga kasashe sama da 80, kuma kudaden da yake samu a duk shekara na kai wa sama da dala biliyan $26, yayinda AB InBev kuma yake da ma'aikata 155,000 kuma tana da hannun jarin sama da dala $47.

Kamfanonin biyu basu tsayar da ka'idojin yarjejeniyar ba tukunna, amma sun kayyade ranar karshe da za a kammala hadin gwiwar a birnin London zuwa 28 ga watan Oktoba.