Dan Biritaniya zai sha bulala 360 a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto Kirsten Piroth

Za a yi wa wani dan Biritaniya mazaunin Saudiyya bulala sama da 360 saboda ya mallaki giyar da ya hada da kan shi a gidan sa.

Tuni dai Karl Andree mai shekaru 74, ya shafe shakera daya a gidan yari bayan an kama shi da kwalaben giya guda shida a but din motarsa.

Iyalan Mr Andree sun ce hukumomin Saudiyya sun sa su sun yi zaton cewar ba za a yi masa bulalar ba saboda shekarunsa da kuma rashin lafiyar da yake fama da ita.

Amma kuma suna fargabar za a iya sake shawara.

Gwamnatin Biritaniya ta nemi a sake shi ba tare da bata lokaci ba.