An kama masu kutsen kwamfuta 'yan China

'Yan sandan China sun tsare masu kutsen kwamfuta bayan da gwamnatin Amurka ta samar musu da jerin sunayen wadanda ake zargi da aikata kutsen kwamfuta, kamar yadda jaridar Washington Post ta ruwaito

An yi imanin cewa masu kutsen sun sace bincike da bayanan cigaba daga kamfanonin Amurka da dama

Wannan kamu na zuwa ne jim kadan kafin Shugaban Kasar China Xi Jinping ya kai ziyara Amurka domin tattaunawa a kan wannan matsala ta tsaron kwamfutoci

China da Amurka a lokuta da dama sun rika zargin juna game da wadanda ke da alhakin matsalar da suka fama da ita ta satar bayanai ta Kwamfuta

An yi imanin cewa wannan kamu da 'yan sandan China su ka yi shi ne na farko da China ta kaddamar bisa bukatar Amurka

Susan Rice, mai bai wa kasar Amurka shawara kan sha'anin tsaro, ta ce wadannan hare hare na kwamfuta na kawo cikas a dangantakar dake tsakanin kasashen biyu