Rikici na karuwa a birnin Kudus

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Zaman dardar na karuwa tsakanin Falasdinawa da 'yan Isra'ila

Tashin hankali na karuwa a birnin Kudus bayan kisan da aka yi wa 'yan Isra'ila uku, kuma aka jikkata wasu da dama yayin wasu hare-hare.

Tashin hankali mafi muni dai shi ne, a wata mota kirar bas inda Falasdinawa biyu, daya dauke da karamar bindiga, dayan kuma dauka da wuka suka kashe mutane biyu, kuma suka jikkata akalla mutane goma.

'Yan mintuna bayan nan wani kuma wani maharin ya aukawa wani wurin shiga bas a birnin Kudus, daga bisani kuma ya aukawa mutanen dake wurin da wuka.

Sannan an kashe wani Bafalasdine a Bethlehem sakamakon arangama da jami'an tsaro a gabar yamma da kogin Jordan.

Hakanan kuma an kai wani harin da wuka a wata unguwa da ke wajen birnin Tel Aviv.

A wannan watan an samu karuwar dabe-daben wuka yayin da rikici tsakanin 'yan Isra'ila da Falasdinawa ya karu.

Firai ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi kiran wani taro na majalisar tsaron kasar inda za su tattauna kan tsauraran matakan da za'a dauka.