'Yar Mali ta bude shafin Facebook saboda alhazai

Hakkin mallakar hoto facebook

Wata mata 'yar kasar Mali ta bude wani shafin facebook a kokarin taimakawa wajen gano abin da ya faru ga mahajjata dari biyu 'yan kasar Mali da har yanzu ba'a san inda suke ba tun bayan turmutsutsun da aka samu a lokacin aikin hajjin bana.

Matar wadda ke zaune a Faransa ta nemi iyalan mutanan da su aika mata hotuna da sunayen 'yan uwansu da ba'a jiduriyarsu ba wanda ita kuma ta ke sakawa a shafin na Faceboook.

Ta ce ta bude shafin ne saboda ba bu wani abin a zo a gani da aka yiu domin gano mahajjatn kasar ta Mali.

Jami'ai a Bamako, babban birnin kasar Malin sun ce 'yan kasar sittin ne suka rasu yayin da ba a ga kimanin dari biyu ba.