Za a gabatar da rahoto kan jirgin MH17

Hakkin mallakar hoto REUTERS
Image caption Jirgin na dauke da mutane sama da 200 a lokacin da ya fado

A ranar Talata ne ake sa ran gabatar da rahoto kan faduwar jirgin saman Malaysia mai lamba MH-17, wanda ake zargin an harbo a gabashin Ukraine a watan Yulin shekarar 2014.

Ana sa ran hukumar kiyaye hadurra ta Holan za ta tabbatar da cewa wani makami mai linzami ne ya kakkabo jirgin, wanda ya taso daga birnin Amsterdam zuwa Kuala Lumpur amma ba a tsammanin za a bayyana wanda ya harbo jirgin.

Rahoton zai kuma duba dalilin da ya sa aka dauki kwanaki hudu cur kafin a tabbatarwa mutane cewa akwai 'yan uwansu a cikin jirgin.

Yawancin fasinjojin da ke cikin jirgin 'yan kasar Holan ne.