An kashe 'yan bindiga 2 da soja 1a Okene

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Sojojin Najeria a wani fareti

Soja 1 ne da 'yan bindga 2 suka mutu a arangamar da aka yi a garin Okene na jihar Kogi.

An kuma kama bindigogi da albarusai da kuma wani babban bom a binciken da jami'an tsaro su ka yi a wani masallaci a Enike.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Kanar Usman Kuka Sheka Kakakin rundunar sojin a hirarsa da BBC.

Tun ranar Litinin ne aka yi arangama tsakanin jami'an tsaro da wasu 'yan bindiga a garin.

Rahotanni farko sun ce an wayi gari tare da jin karar harbe-harbe abin da ya tilasta wa al'ummar garin kasancewa a cikin gidajensu.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kogi, Ogye Aya Williams ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce sojoji ne suka kai samame domin damke wani wanda ake zargi da aikata laifi.

A karshen watan da ya wuce ma wasu 'yan bindiga sun kai hari kan ofishin 'yan sandan farin kaya (watau SSS) da ke Lokoja inda dan sanda daya ya rasa ransa sannan aka kashe 'yan bindiga uku.

A baya dai an sha yunkurin balle gidan yarin birnin Lokoja domin sakin 'yan Boko Haram din da ake tsare da su a ciki.

Jihar Kogi na daga cikin jihohin da ake samun tashe-tashen hankula wadanda ke da nasaba a kungiyar Boko Haram.