Majalisa ta jinkirta tantance Amaechi

Hakkin mallakar hoto Amaechi Twitter
Image caption Amaechi na fuskantar kalubale

Majalisar dattawan Nigeria ta jinkirta tantance tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Ameachi daga ranar Laraba zuwa ranar Alhamis.

Matakin ya biyo bayan rashin mika rahoton kwamitin da'a da korafe-korafen jama'a na majalisar dattawan da ke binciken korafi a kan Mr Amaechi.

Shugaban kwamitin, Sam Anyanwu, ya shaida wa majalisar cewar ba su kamalla rubuta rahotonsu ba a kan binciken da suka gudanar a kan Amaechi.

Kenan a ranar Laraba, majalisar za ta tantance mutane tara ne daga cikin sunayen da shugaba Muhammadu Buhari ya aike mata.

Sanatoci uku daga jihar Ribas sun nuna adawa da yunkurin bai wa Amaechi minista saboda suna zarginsa da wawure kudaden al'umma a lokacin yana gwamna.