Ana tuhumar Apple da satar fasaha

Hakkin mallakar hoto AFP

Wakila kamfanin Apple ya biya tarar dala miliyan 862 bayan da ya kasa samun nasara a gaban wata kotu kan tuhumar da ake yi masa na satar fasaha.

Jami'ar Wisconsin na tuhumar kamfanin Apple da satar fasaharta da ya yi amfani da su a cikin wasu wayoyinsa na Iphones da kuma Ipads.

A shekarar 1998, jami'ar ta shigar da kara gaban kotu domin ta inganta abubuwan da suka kunshi kwalwakwar kwamfuta da ake kira microchips.

Ana zargin kamfanin Apple da amfani da fasahar a wayoyinsa na iphone 5 da 6 da kuma 6plus .

Haka kuma jami'ar ta Wisconsin ta shigar da kara gaban kotu inda ta ke tuhumar kamfanin Intel da satar fasaharta a shekarar 2008.

Sai dai daga bisani bangarorin biyu sun sasanta a wajen kotu a kan kudin da ba a bayyana ba.

A cikin takardun kotun jami'ar ta yi zargin cewa kamfanin Apple ya yi watsi da kiraye kirayen da ta dinga yi masa a kan bukatar samun lasisin amfani da fasaharta ko dayake abin da haka ke nufi shi ne zai cigaba da biyan jami'ar kudi.

Jami'ar ta kara da cewa kamfanin Apple ya sabawa kaida kuma abu ne da zai iya sa kotu ta ci sa tara idan ta sameshi da laifi.

Bayan kotu ta kamala saurar sannan za a san yawan kudin da kamfanin Apple zai biya.