Dole a dauki mataki a kan Putin — Clinton

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hillary ta ce ba za a amince da lugudan wutar da Putin ke yi a Rasha ba

'Yan takarar shugabancin Amurka su biyar a karkashin jam'iyyar Democrat, sun gudanar da mahawararsu ta farko gabanin zaben da za a yi a badi.

Daya daga cikin su, Hillary Clinton, da kuma Sanata mai cin gashin kansa, Bernie Sanders sun tafka muhawara mai zafi game da manufar Amurka a kasar Syria da dokokin mallakar bindiga da kuma tattalin arzikin kasa da kuma farmakin da Rasha take kai wa a Syria.

Hillary Clinton ta ce lokaci ya yi da za a tashi tsaye, ga abin da ta kira cin zalin da Shugaba Putin na Rasha ke yi.

Ta ce, "Ina tunanin yana da muhimmanci Amurka ta fito fili ta bayyanawa Putin cewa ba za a amince ya kasance cikin Syria ba inda yake haifar da karin rudani, da yi wa jama'a ruwan bama- bamai a madadin Shugaba Assad".