Zaman dar-dar na karuwa a birnin Kudus

Hakkin mallakar hoto Getty

'Yan sanda a birnin Kudus sun harbe Falasdinawa biyu har lahira a wasu hare-haren daban-daban da suka kai kan wasu Isra'ilawa a birnin.

Lamarin ya faru ne sa'o'i bayan da Isra'ila ta tura daruruwan sojoji a duk fadin kasar, domin taimakawa 'yan sanda shawo kan hare-haren bindiga da wuka da Falasdinawa ke kai wa.

Gwamman Falasdinawa da ke zanga-zanga a Bethleham a gabar tekun yammacin Jordan ne suka yi arangama da dakarun sojin Isra'ila.

An kashe Isra'ilawa bakwai a hare haran da aka fara kaiwa tun daga farkon watan Oktoban nan.

Yayin da aka kashe Falasdinawa akalla talatin, da suka hada da mutanen da ake zargi da kai hari da kuma kananan yara bakwai.