Sojin Isra'ila na shirin tunkarar Falasdinawa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojin Isra'ila za su rufe wasu yankunan birnin Qudus.

Rundunar sojin Isra'ila ta fara aikawa da daruruwan dakarunta zuwa birane daban-daban na kasar domin taimaka wa 'yan sanda su murkushe Palasdinawan da ke kai hare-haren bidigogi da wukake a 'yan kwanakin nan.

A gabashin birnin Kudus, an bayar da umarnin kafa wuraren binciken abubuwan hawa, ko da ya ke ba a kafa su a yankunan Palasdinawa ba, inda ake samun yawancin hare-haren.

An fara daukar matakin ne sakamakon amincewar da gwamnati ta yi ta bai wa 'yan sanda damar rufe wasu yankuna na gabashin birnin Kudus.

Kazalika, hukumomin na da damar rushe gidajen Falasdinawan da ke kai hare-hare a kan Yahudawa, sannan a hana su 'yancin ci gaba da zama a birnin Kudus.

An ci gaba da rikice-rikice a yankin ne sakamakon kwana da kwanakin da aka kwashe ana zaman zulumi a kan samun damar shiga Masallacin Al-Aqsa mai muhimmanci da Musulmai da Yahudawa.