Za a tsagaita wuta a Myanmar

Kwafi na yarjejeniyar tsaigata wuta ta kasar Myanmar
Image caption Kwafi na yarjejeniyar tsaigata wuta ta kasar Myanmar

Gwamnatin kasar Myanmar ta ce ta rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ta da kungiyoyin mayakan sa-kai guda takwas na kasar.

Sai dai kungiyar 'yan tawayen da ta fi kowacce kaurin-suna ba ta cikin jerin kungiyoyin da aka cimma yarjejeniyar da su.

An gudanar da bikin rattaba hannun ne a Neipido, babban birnin kasar, bayan shekaru biyu da aka kwashe ana neman bakin-zaren kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar.

Wannan dai shi ne matakin karshe da gwamnatin Myanmar ke fatan zai kawo wa kasar zaman lafiya mai dorewa.