An amince da ministocin Nigeria 18

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Wasu daga cikin ministocin da aka amince da su

Majalisar dattawan Nigeria ta tantance sannan kuma ta amince da mutane 18 domin shugaba Muhammadu Buhari ya nada su a matsayin ministoci.

Shugaban majalisar, Sanata Abubakar Bukola Saraki shi ne ya jagoranci zaman wanda aka amince da ministocin daya bayan daya.

Tun a ranar Talata majalisar dattawan ta tantance mutane 10 sannan kuma a ranar Laraba ta tantance mutane 8 inda jumlar ta zama mutane 18.

Majalisar dattawa ta jinkirta tantance tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Ameachi sai zuwa ranar Alhamis.

Matakin ya biyo bayan rashin mika rahoton kwamitin da'a da korafe-korafen jama'a na majalisar dattawan da ke binciken wani korafi a kan Mr Amaechi.

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike wa majalisar sunayen mutane 37 ne domin ya nada su a matsayin ministoci kafin daga bisani ya janye sunan Alhaji Ahmed Ibeto daga jihar Niger.

Ga jerin wadanda aka amince da su:

 1. Sanata Udoma Udo Udoma daga jihar Akwa Ibom
 2. Kayode Fayemi daga jihar Ekiti
 3. Audu Ogbeh daga jihar Benue
 4. Ogbonayya Onu daga jihar Abia
 5. Osagie Ohanire daga jihar Edo
 6. Laftar Janar AbdulRahman Dambazau daga jihar Kano
 7. Alhaji Lai Muhammed daga jihar Kwara
 8. Hajiya Amina Mohammed daga jihar Gombe
 9. Injiniya Sulaiman Adamu daga jihar Jigawa
 10. Alhaji Ibrahim Usman Jibrin daga jihar Nasarawa
 11. Babatunde Raji Fashola daga jihar Lagos
 12. Ibe Kachukwu daga jihar Delta
 13. Alhaji Abubakar Malami daga jihar Kebbi
 14. Hajiya Aisha Alhassan daga jihar Taraba
 15. Solomon Dalong daga jihar Filato
 16. Chris Ngige daga jihar Anambra
 17. Hadi Sirika daga jihar Katsina
 18. Kemi Adeosun daga jihar Ogun