'An yi wa Sankara ruwan harsasai'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Afrika tana wa Thomas Sankara kallon jarumin ta, inda aka yi masa inkiya da 'Che Guevara'.

Lauyan iyalan tsohon shugaban kasar Burkina Faso, Thomas Sankara, ya ce binciken da aka gudanar a kan gawar marigayin, ya nuna cewa an yi mata ruwan harsasai.

Lauyan ya kara da cewa har yanzu iyalan na jiran gwajin da zai tabbatar masu da cewa gawar tasa ce.

An yi hanzarin binne jarumin nahiyar Afrikan, wanda aka yi wa lakabi da 'Che Guevara', bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a shekarar 1987.

Ba a bayar da damar tono gawar ba a shekaru 27 da Blaise Compaore, tsohon shugaban da aka hambarar a wata tarzoma a shekarar da ta gabata, ya kwashe yana mulki.

Mr Compaore ya jima yana musanta zargin da ake masa cewa yana da hannu a kisan da aka yi wa Sankara, inda yake ta nanata cewa komai a fili yake kuma bashi da wani abu da yake boyewa, duk da cewar lokacin da yake mulki kotu ta toshe duk wata hanya ta yunkirin da iyalan Sankara suka yi domin a tono gawar.

Ambroise Farama, daya daga cikin lauyoyin iyalan Sankara, ya ce abubuwan da aka gano a binciken gawar na da ban mamaki kwarai da gaske.