'Attajiran China sun wuce na Amurka'

Wani kamfanin bincike ya ce a karon farko, hamshakan attajiran da su ka kai matsayin biloniya a China sun wuce na Amurka.

Rahoton na kamfanin Hurun, da ke Shanghai ya ce a yanzu China tana da attajiran suka kai matsayin biloniya su 596 a yayin da Amurka ke da biloniya 537.

Yawan attajiran China na ci gaba da karuwa duk da koma baya da tattalin arzikin kasar ke fuskanta.

Rahoton Hurun ya ce akwai wuya wajen tattara alkaluman masu hannun da shuni kuma watakila adadin a zahiri ya nunka abin da aka wallafa.