An sabunta dokar ta-baci a Diffa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Boko Haram ta yi barna a Diffa

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sabunta dokar ta-baci a yankin Diffa domin murkushe hare-haren kungiyar Boko Haram.

Kungiyar ta kashe fiye da mutane 40 a yankin Diffa, kusa da kan iyakar kasar da Najeriya a makonni kadan da suka wuce.

'Yan gudun hijira kimanin 150,000 daga Najeriya ne ke zaune a yankin domin tserewa hare-haren da Boko Haram ke kai musu.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa Boko Haram ta kai hare-hare sau 57 a yankin na Diffa tun daga watan Fabrairu.

A baya ma dai, hukumomi a Jamhuriyar ta Nijar sun sanya dokar ta-baci a yankin.

Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi sun kafa runduna ta hadin gwiwa domin kawar da kungiyar Boko Haram.