Ana fama da karancin abinci a Madagascar

Image caption Yaran tsibirin Madagascar na tsinbirewa sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

Tsibirin Madagascar na fuskantar matsalar karancin abinci mai gina jiki ga yara, lamarin da ya shafi kimanin kashi 50 cikin 100 na yaran.

Wannan karancin abinci ya sa yaran suna tsinbirewa duk da yawan shekarun su.

Abin da ya fi daure wa mutane kai shi ne yadda aka yi yaran ke fuskantar karancin abinci har ya kai ga shafar kwakwalwarsu, bayan ana noman abinci, akwai kuma da abubuwan more rayuwa, sannan talauci bai tsananta a kasar ba.

Yanzu dai an fara zurfin tunanin domin gano dalilai daban-daban da suka sa ake fama da karancin abinci mai gina jiki a tsibirin.