Turkiyya ta jaddada bukatar shiga Tarayyar Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Turkiyya, Tayyip Erdogan

Turkiyya ta ce za ta saurari shirin Tarayyar Turai kan magance kwararar 'yan gudun hijra idan za a biya bukatunta na shiga Tarayyar.

Shugabannin kasashen na Tarayyar Turai dai za su yi taro ranar Alhamis a Brussels a kan yadda za su hada gwaiwa da Turkiya domin magance matsalar 'yan gudun hijira.

Sai dai Turkiyyar ta ce kafin ta amince da bukatun na tarayyar turai tana da nata bukatun da take so a biya mata, wadanda suka hada da neman tallafin kudi da batun biza da kuma neman zama mamba a Tarayyar Turan.

Ana dai tunanin cewa sama da 'yan gudun hijira miliyan biyu ne a kasar ta Turkiyya wadanda suka fito daga Syria.