Sabon rikici ya barke a Allepo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Birnin Aleppo ya daidai ce

Dakarun gwamnatin Syria tare da goyon bayan Rasha sun bude wuta kan mayakan 'yan tawaye a birnin Aleppo.

Hakan na zuwa ne bayan da Turkiyya ta ce ta kakkabo wani jirgi marar matuki a sararin samaniyarta.

Gwamnatin Syria ce ke iko da wani bangare na Aleppo a yayin da 'yan tawaye ke iko da wani bangaren birnin.

Mayakan IS da wasu 'yan tawayen ne ke yaki domin kawar da Shugaba Bashar al-Assad.

Wasu majiyoyin soji sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akwai daruruwan mayakan Hezbollah da na Iran da ke cikin wannan sabon tashin hankalin.