An kama mata 62 saboda sanya nikabi a Chadi

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'Yan sanda sun ce dole ne matan su biya tarar $170 kafin a sake su.

'Yan sanda a kasar Chadi sun tsare mata 62 saboda sun sanya niqabi a bainar jama'a a daidai lokacin da kasar ke tsaurara tsaro sakamakon hare-haren 'yan ta'adda.

Kakakin rundunar 'yan sandan kasar, Paul Manka, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa an kama matan ne a N'djamena, babban birnin kasar saboda keta dokar hana sanya niqabi da suka yi.

A cewar sa, matan za su biya tarar $170 kafin a sake su, yana mai cewa idan aka sake kama su sanye da niqabi, za a tuhume su da taimakawa masu tayar da kayar ba.

A watan Yuni ne hukumomi a kasar suka sanya dokar hana sanya niqabi domin dakile hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa a kasar.

Kungiyar dai tana yin amfani da kananan yara da mata domin tayar da bama-bamai a kasar ta Chadi da Najeriya da Kamaru da kuma Jamhuriyar Nijar.