Matashi ya kashe mahaifansa a Enugu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Matashin ya yi amfani da adda wajen kisan

Wani matashi da ake zaton yana da tabin hankali ya kashe mahaifansa da makwabtansu guda tara a jihar Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya.

An ce dai matashin ya hau iyayen nasa da sara ne da adda, bayan kuma ya kashe su sai ya nemi ashana ya banka wa gidan wuta.

Daga nan kuma sai ya shiga gidan makwabta a inda ya kashe mutane tara da suka hada da kananan yara.

Yanzu haka rundunar 'yan sandan jihar ta Enugu ta baza komarta wajen neman matashin.

Sai dai kuma kwararru kan halayyar dan adam sun ce watakila matashin na da tabin hankali.