Burtaniya ta sayar wa Uganda da fasahar sa-ido

Hakkin mallakar hoto Getty

Wasu da takardu da sashen Newsnight na BBC ya bankodo sun nuna cewa wani kamfanin kasar Burtaniya ya sayar wa kasar Uganda da fasahar sa ido da aka yi amfani da ita wajen murkushe abokan hamayya na shugaban kasar tare kuma da yi mu su zamba cikin aminci.

Wani rahoto na cikin gida ya yi zargin cewa an yi amfani da fasahar a wasu kasashen nahiyar Afrika da kuma Syria.

Sai dai gwamnatin Uganda ta musanta zargin.

Kamfanin da ake kira Gamma group, ya ce ba ya taimakawa ko karfafa gwiwar duk wata cibiyar gwamnati wajen amfani da kayayyakinsa.

Alhaki ya rataya a kan wuyan kamfanonin fasaha wajen ganin ba su sayar da na'urorinsu ga kasashe idan suna da damuwa a kan yadda za a yi amfani da su.

Sai dai babu ka'idojin da suka gindaya yadda za a sayar da na'urar sa - ido kamar yada ake da su a kan makamai ko da yake an samu wasu 'yan Majalisar dokokin Burtaniya da kuma kungiyoyin kare hakkin bil'adama da suka nuna damuwa.

Suna fargabar cewa za a iya amfani da fasahar wajen murkushe abokan hamayya a kasar ta Uganda.

BBC ta yi aiki tare da kamfanin Privacy international, wadanda suka bankado takardun sirri da kuma wasu takardu da suka yi cikakken bayani a kan yadda aka yi amfani da fasahar sa ido wajen murkushe bore ko tawaye a cikin kasar ta Uganda