Bishop-Bishop za su rungumi 'yan hijira a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Bishop bishop din sun ce za su tattauna da majami'u domin trabar masu hijrar.

Bishop-Bishop na cocin Ingila sun yi kira ga gwamnatin Biritaniya da ta amince da karbar karin 'yan gudun hijira 30,000 daga kasar Syria.

Hakan dai yana nufin kari a kan 20,000 din da Biritaniyar ta bai wa mafaka har na tsawon shekaru biyar.

Sun yi wannan kiran ne a wata wasikar sirri da suka aike wa da firai ministan kasar David Cameron, a watan da ya gabata, bukatar da kuma a yanzu suka bayyana ta a fili.

Wasikar dai ta ce masu gudun hijira suna bukatar kulawa ta musamman duba ga irin wahalar da suke fuskanta.

Bishop-Bishop din 84 ne daga cikin 108 suka goyi bayan wannan bukatar, har ma suna cewa za su nemi yardar majami'u domin tarbar 'yan gudun hijirar.