Geidam: Mutane suna barin garin

Hakkin mallakar hoto Screengrab
Image caption 'Yan Boko Haram sun sha kai hari a Geidam

A Najeriya rahotanni na cewa, jama'a na guduwa daga garin Geidam na jihar Yobe sakamakon fargabar yiwuwar sake fuskantar harin 'yan Boko Haram.

Wani mazaunin garin ya ce, yawanci mata da yara kanana ne ke ficewa daga garin kuma harkoki sun ragu sosai a garin.

Koda a wannan makon kasuwar garin ba ta ci ba saboda fargabar tsaro.

Hakan na faruwa ne sama da mako guda bayan 'yan Boko Haram sun kai hari garin na Geidam ranar da kasuwa ke ci inda rahotanni suka ce sun yi awon gaba da kayan abinci mai dumbin yawa.

Tuni dai rundunar sojan Najeriya ta karfafa samar da tsaro a garin na Geidam inda aka samar da karin dakaru da kuma kayan aiki, da kuma bada tabbacin tabbatar da tsaro.