Jamus: An daba wa 'yar takara wuka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Jamus dai tana goyon bayan karbar 'yan gudun hijira

Wani mutum dauke da wuka ya yi kukan kura ya aukawa 'yar takarar magajin garin birnin Koln na Jamus kwana guda kafin zabe.

A yanzu haka 'yar takarar , tana jinyar daba mata wuka da mutumin ya yi a wuya.

Kazalik, wasu mutanen hudu sun jikkata, dayansu ma yana cikin mawuyacin hali.

Wani babban jami'in gwamnati ya ce, mutum da ya kai harin yana da wata manufa ta siyasa.

Wasu rahotanni na cewa, mutumin ya fadawa 'yan sanda yana adawa da manufar gwamnatin Jamus ta karbar 'yan gudun hijira.