Za a yi bincike kan wanda ya kashe mahaifiyarsa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Shugaban hukumar 'yan sandan Najeriya Solomon Arase

Hukumomin tsaro a jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Nijeriya, sun bayyana cewa sun fara gudanar da bincike kan abin da ya faru, da ya kai ga wani mutum ya kashe maihaifiyarsa mai kimanin shekaru 80, ta hanyar sassara ta da adda a ka.

Lamarin kisan wanda tuni ya jefa jama'a cikin zullumi da ta'ajibi, ya faru ne a Unguwar Janta Mangoro da ke Jos, babban birnin jihar ta Filato, a ranar Alhamis.

Bayan faruwar lamarin, sai matasa suka kama mutumin da ake zargi mai shekaru 52, yayin da yake yunkurin tserewa, suka yi masa dukan kawo wuka, kana suka daure shi, kafin daga bisani jami'an tsaro suka dauke shi zuwa asibiti domin farfado da shi.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Filato DSP Abuh Emmanule, ya shaida wa BBC cewa "doka zata yi halinta a kansa, tabbas za a gurfanar da shi a kotu, domin kashe mutum, ba karamin laifi ba ne."

To sai dai kuma bayanai na cewa dama mutumin mai suna Mista Bravo Kunde, ya jarabtu da shaye-shayen kwayoyi da barasa, kuma kan haka ne a kullum mahaifiyar tasa ke yi masa fada da nasiha don ya daina, amma kuma ya kan nuna mata bacin ransa kan nasihar da take masa.