Wani mutum ya kashe mahaifiyarsa a Filato

Babban spetan 'yan sanda  Najeriya Hakkin mallakar hoto Nigeria Police website
Image caption Babban spetan 'yan sanda Najeriya

Hukumomin tsaro a jihar Filato dake arewa ta tsakiyar Nijeriya, sun bayyana cewa sun fara gudanar da bincike kan wani mutum da ya kashe maihaifiyarsa mai kimanin shekaru tamanin, ta hanyar sassara ta da adda a ka.

Lamarin kisan wanda tuni ya jefa jama'a cikin zulumi da ta'ajibi, ya faru ne a unguwar Janta Mangoro da ke Jos, babban birnin jihar ta Filato, a ranar Alhamis.

'Yan sanda sun ce ba su san dalilin da yasa mutumin ya kashe mahaifiyarsa ba amma zasu binciki lamarin

Lamarin na zuwa bayan wani matashi da ya kashe mahaifinsa da kuma wasu mutune 9 a jihar Enugu a ranar Talata.

Wasu masana halayyar 'dan Adam sun ce akwai bukatar duba hankali da kuma tunanin masu irin wanannan aika-aikar