Za a fara rijistar Fulani a Nigeria

Image caption Ana yawan samun rikice-rikice tsakanin Fulani da sauran kabilu a Najeriya

Shugabannin Fulani a yankin kudu maso yammacin Najeriya sun za su yin rijistar Fulanin da ke kiwon dabobbinsu a yankin domin magance rikice-rikice.

Shugabannin sun ce yin rijistar zai sa a san kowanne Bafillatani da inda ya fito da kuma wajen da yake gudanar da kiwonsa domin samun bayani kansu a duk lokacin da ake zarginsu da abin da bai dace ba.

Wannan ya zo ne bayan samun rashin jituwa tsakanin Fulani makiyaya da Yarbawa manoma a sakamakon sace tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Cif Olu Falae, wanda sai bayan wasu kwanaki aka sako shi.

Lamarin dai ya janyo kungiyar Yarabawa zalla ta Afenifere ta soma yin kiran Fulani su fice daga yankinsu.

An sha samun rikice-rikice tsakanin Fulani da Makiyaya a jihohi daban-daban na Najeriya wanda haka ke zama barazana ga tsaron kasa a wasu lokutan.