Bala'in ruwa da iska ya afkawa Philiphines

Hakkin mallakar hoto APTN

Mahaukaciyar gugguwa da aka yi wa lakabi da Koppu da ke dauke da ruwa da iska mai tafiyar kilomita 200 a cikin sa'a guda ta afkawa tsibirin Luzon da ke kasar Philiphines .

Ana sa ran samun ambaliyar ruwa da zaftarewar laka a cikin kwanakin uku da za a sheka ruwa a tsibirin.

An dai dakatar da zirga- zirgar jiragen sama kuma an rufe hanyoyi kuma an kwashe duban mutane da ke zama a wuraren da ke kusa da bakin teku.

A ranar Juma'a shugaba Benigno Aquino ya nemi alummar kasar a kan su kasance cikin shirin ko ta kwana , wanda shi ne karon farko da zai yi haka tun bayan da mahaukaciyar guguwa ta Haiyan ta afkawa kasar a shekarar 2013.