Ci gaban tattalin arzikin China ya ragu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cibiyar harkokin masana'antu a China

Sababbin alkaluman tattalin arziki da China ta fitar sun nuna yadda ci gaban tattalin arzikinta ya fi kowanne lokaci tafiyar hawainiya a yanzu, tun da aka shiga matsalar tattalin arziki a duniya a shekaru shida da suka gabata.

Alkaluman da aka fitar a zango na uku a shekara, sun yi kiyasin cewa tattalin arzikin China zai rika karuwa ne yanzu da kashi 6.9 cikin dari.

An samu jinkiri a ci gaban tattalin arzikin kasar ne duk da yadda kasar ta yi ta rage kudin ruwa, tare kuma da bullo da wasu matakai na raya tattalin arzikin.

Sai dai duk da girman tafiyar hawainiyar, matsalar ba ta yi munin da masana suka yi hasashe a farko ba.

Wadannan alkaluma da aka fitar, su ne suka fara tabbatar da fargabar da masu zuba jari suke yi, tun bayan da kasuwannin hannayen jari a China suka ja baya, yayin da kuma aka rage darajar kudin kasar a watan Agusta.

Kasancewar Chinan ta daya a duniya a fannin saye da sayar da hajoji, kuma babbar kasuwa ga ita kanta, kasar tana taka muhimmiyar rawa ga tattalin arzikin duniya.