Boko Haram ta kashe mutane 11 a Madagali

Hakkin mallakar hoto Screengrab
Image caption Mayakan Boko Haram

A Najeriya, wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane 11 a kauyen Dar da ke karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa.

Mazauna garin sun ce maharan -- wadanda suka hada da mata 'yan kunar bakin wake -- sun isa kauyen ne ranar Asabar da misalin karfe takwas da rabi na dare.

Wani tsohon shugaban karamar hukumar Madagali, Mista Maina Ularamu, ya shaida wa BBC cewa daga cikin maharan, 'yan kunar bakin wake mata su suka fara tayar da bama baman da ke jikinsu inda suka kashe mutanbakwai.

Ya kara da cewa bayan mutane sun firgita sun shiga daji ne sai sauran maharan maza suka rika harbinsu da bindigogi inda suka kashe mutane hudu.

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar, NEMA ta tabbatar da kai harin, amma ta ce ba ta da cikakken bayani a kai.