Batun iskar gas tsakanin Nigeria da Ghana

Image caption Matsalar rashin wutar lantarki na daya daga cikin kalubale da kasar Ghana ke fama da shi.

Kasar Ghana tana shirin kulla wata yarjejeniya da Najeriya ta sayen iskar gas a kan kusan $103m bayan kamfanin gas da ke Najeriyar ya janye aniyarsa ta hana bai wa Ghana isakar gas din.

Ghana ta sha gwagwarmaya wurin biyan kudin iskar gas din da take saye daga Najeriya tun bayan da kamfanin samar da wutar kasar Volta River Authority (VRA) ya shiga halin rashin kudi sakamakon daina aron kudi bankin da ta yi saboda kudin ruwan da ake tsawwalawa.

Kamfanin VRA ya daina biyan Najeriya kudin iskar gas tun watan Agustan bara, amma gwamnatin Ghana ta biya $10m a makon jiya, hakan kuma ya bude hanya domin tattaunawa game da tsarin da za a bi wurin biyan sauran bashin.

Kamfanonin samar da wutar Ghana na cikin matsala sakamakon karancin kudi da rashin kayan gudanar da ayyuka a kogin kasar da kuma satar wutar lantarki da 'yan kasar ke yi.

Ana amfani da iskar gas din aka zuko daga Najeriya, ta hanyar kasashen Benin da Togo, wurin samar da kashi daya cikin hudu na wutar lantarkin Ghana, dalilin haka kuwa katse wutar zai iya janyo wa kasar koma baya.

Matsalar kuma za ta iya shafar siyasar shugaba John Mahama, wanda ya sha alwashin kawo karshen matsalar wutar lantarki a Ghana kafin farkon shekarar 2016.