An tantance karin ministocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption A lokacin da Hajiya Khadija ke jinjina wa sanatoci

Majalisar dattawan Najeriya za ta ci gaba da tantance mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya tura mata domin nada su ministoci.

Mutane biyun da majalisar ta tantance a ranar Talata su ne Barrister Adebayo Shittu daga jihar Oyo da kuma Khadija Bukar Ibrahim daga jihar Yobe.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan, Sanata Ali Muhammad Ndume ya ce a ranar Laraba za su tantance tsohon gwamnan jihar Ribas, Mr Rotimi Amaechi.

A makon jiya dai majalisar ta tantance, tare da amincewa da nadin mutane 18 daga cikin mutane 36 da shugaban ya tura sunayen su ga 'yan majalisar.

Sai dai majalisar ta karbi korafe-korafe a kan wasu daga cikin wadannan mutanen.

Daga cikin su har da tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amechi da Aisha Abubakar daga jihar Sokoto da kuma Hajiya Khadijah Abba Ibrahim daga jihar Yobe.