Kazamin fada ya barke a Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan kungiyar IS

Rahotanni na cewa ana gwabza kazamin fada a filayen daga a tsakiya da kuma gabashin Syria.

Dakarun gwamnati da kuma kawancen mayakan sa-kai da Rasha ke goyon baya sun kaddamar da hare-haren sama, suna kuma kokarin kai wa ga sansanonin 'yan tawaye a akalla larduna biyar.

Tun da farko da yake magana a taron manema labarai a Madrid, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ce yana shirya ganawa da shugabannin Rasha da Turkiya da Saudiyya da kuma Jordan domin kokarin gujewa abin da ya kira rugujewar Syria baki daya.

Ya ce "Shugaba Obama ya bayyana a fili cewa yana ganin kasarmu ke da alhakin yin iyakar kokari domin gujewa durkushwar Syria baki daya da kuma kaucewa duk wani kalubale da zai hana aiwatar da hakan."