Makahon dan Jarida a Somali

Abdifatah Hassan, makaho dan jarida ne kuma dan kasar Somalia da ke zaune a Mogadishu babban birnin kasar, ya yi sha'awar zama dan jaridar tun a yarintarsa.

Ya yi ta kokari wajen samun ilimin da zai taimaka masa wajen zama dan jaridan.

Bayan ya shafe shekaru yana nuna kwazo, sai Abdifatah yaga ya shiryawa soma yin aikin.

Duk da cewar Abdifatah makaho ne, bai taba fitar da ran cewar wata rana zai samu damar yin aikin ba, inda zai nuna kwazonsa.

"Na yi rashin lafiya ne bayan an haife ni, kuma sai ya taba idanu na.Amma sai ya ce ba hujja ba ce da za ta hana shi bin abin da ransa ya ke so ba," in ji Abdifatah.

A shekarar 2002, sai yayi niyyar fara ikin jaridar.

Amma kuma abubuwa ba su zo masa cikin sauki ba saboda babu gidan jaridar da ke son ta dauke shi aiki.

'Yanke kauna'

A cewarsa, duk gidajen jaridun sun yi zaton cewar babu yadda za a yi makaho ya taka wata muhimmiyar rawa a matsayin dan jarida.

"Duk gidajen jaridu da na nemi aiki a wurinsu ba su yadda da ni ba". Ban ji dadin hakan ba," in ji Abdifatah.

Amma hakan bai sa ya yi kasa a gwiwa ba, a shawarsa ta yin aikin 'yan jarida wanda zai rika aikewa Somali, wacce ta ke fuskantar rikicin siyasa da rahotanni.

Abdifatah yana so ya cika burinsa domin ya farantawa abokansa duk da dai cewar gidajen jarida basa maraba da masu nakasa.

Duk da wariyar da ya ke fuskanta, Abdifatah baya dora laifi kan halin da ya ke ciki saboda ya yi imanin abu ne daga Allah.

Bayan ya shafe shekaru biyu yana jiran tsammani, a shekarar 2004 sai gidan rediyon Goobjoog Fm da ke Mogadishu suka dauke shi aiki.

Ya ce "Na shafe shekaru biyu ina jira, sai a shekarar 2004 gidan rediyon Goobjoog suka dauke ni aiki."

'Wakili a majalisa'

Tun lokacin a gidan rediyon ya ke yin aiki. An dauke shi a matsayin mai aika rahotanni, daga baya kuma sai aka mayar da shi mai yin labarai da rahotanni a kan zaman majalisa.

Bayan 'yan shekaru sai Abdifatah ya yi ta samun ci gaba a wajen aikinsa kuma sai ake girmama shi.

Abdifatah ya zama mai gabatarwa kuma mai hada wani shiri da ake tattaunawa a kan abubuwan da suka danganci siyasa.

A kullum da kanshi ya ke gudanar da duk wani abu da ya danganci shirin da ake yi kullum amma banda ranar Juma'a.

Ya ce "Ina nemo dan siyasa ne wanda zai yi musu bayani a kan abubuwan da za mu tattauna a shirin kuma sai ya zama shine zai jagoranci shirin."

Shirin Abdifatah shi ne shirin da ake sauraro a gidan rediyon da ya ke aiki saboda ya na kalubalantar 'yan siyasa a kan nauyinsu da kuma irin shawarwarun da suke bayarwa a majalisa.

Duk da cewar aikinsa ya kara masa daraja da kuma farinjini, amma ya kan fuskanci matsala.

A watan Maris na wannan shekarar ne, sashen bincike kan laifuka na Somalia ya dauke shi daga gidan shi ya yi garkuwa da shi har na tsawon kwanaki bakwai.

Ba su yar da iyalansa da abokan aikinsa sun ganshi ba.

Abin da ya jawo suka daga sassan ma'aikatu daban-daban. Amma kuma daga baya sai aka sako shi ba tare da an kama shi da wani laifi ba.

Duk a cewar aikin jarida a Mogadishu na daya daga cikin wuraren da aikin jarida ke da hadari, kuma shirin yana mayayar da hankali ne a kan abubuwan da suka shafi siyasa amma Abdifatah baya tsoro.

Ya ce "Na yarda da nuna kwazo a aiki, dole ne kowa ya fuskanci duk wani abu da Allah ya tsara masa a rayuwa. Ako da yaushe ina taka tsatsan a duk abinda na ke yi domin na kare kaina".