An kara jinkirta tantance Amaechi

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Tun a karshen watan Satumba shugaba Buhari ya soma aika sunayen ministoci

Majalisar dattawan Nigeria a karo na biyu ta kara jinkirta tantance tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi domin a nada shi a matsayin minista.

Tun a makon jiya ne aka sa ran za a tantance Amaechi amma majalisar ba ta yi haka ba duk da cewar ta amince da mutane 18 daga cikin sunaye 36 da Shugaba Muhammadu Buhari yake son ya nada a matsayin ministoci.

A zaman ta na ranar Talata, majalisar ta fitar da jerin sunayen mutane uku wadanda za ta tantance a matsayin ministoci.

Mutanen su ne: Barrister Shittu Adebayo da Claudius Omoleye Daramola da kuma Khadija Abba Ibrahim.

Sai dai Sanata Ali Muhammad Ndume watau shugaban masu rinjaye a majalisar dattawan ya ce a ranar Laraba za su tantance Mr Amaechi.

Da ma dai kan sanatoci ya rabu bayan da wasu sanatoci daga jihar Ribas suka gabatar da takardar koke kan Rotimi Amaechi a matsayin minista.

Hakan dai ya haddasa rudani a zauren majalisar tsakanin wasu 'ya'yan jam'iyyar APC mai mulki da kuma 'yan jam'iyyar adawa ta PDP dangane da amince wa da takardar koken.

Wasu mutanen da ake da korafe-korafe a kansu su hada da; Hajiya Aisha Abubakar daga jihar Sokoto.