Za ku iya fada wa wayar Apple lokacin da ku ka yi jima'i?

Hakkin mallakar hoto AFP

Za ku iya gaya wa mutane lokacin da kuka yi jima'i?

Lokacin da kamfanin Apple ya kirkiro sabon manhajarsa ta i0S9, wacce ke dauke da sabbin na'urori, ciki har ma da yadda mata za su iya lissafa ko sau nawa suka yi jima'i da kuma yanayin haila.

Manhajar 'HealthKit' ce ta farko da aka fara fitowa da ita, wadda ke bibiyar komai, ciki har da alakar fatar jiki da kwayoyin halitta, da kuma yadda sinadarai ke aiki a jikin mutum, amma kuma ba manhajar ba ta da fasahar binciken da sabuwar manhajar i0S9 ke da ita na lokacin jima'i.

An samu wasu manhajoji da aka kirkiro a baya da suka yi yunkurin samun irin fasahar, amma duk da haka, sai da aka soma zargin kamfanin Apple da ma sauran kamfunan wayoyi da rashin maida hankali ga abubuwan da suka shafi lafiyar mata.

Manhajojin lafiya na kamfanin Samsung watau S Health da na Google watau Google Fit, basu kara wannan fasaha ba tukunna, duk da cewar akwai yiwuwar cikin lokaci kalilansu ma za su bi sawu.

Akwai alamomi daban-daban da mata kan yi amfani da wurin fahimtar al'adarsu ta wata, hakan kuma ke sa su gane lokacin da ciki zai fi shiga, dalilin haka manhajar za ta taimakawa mata da ke neman haihuwa da ilimi wurin bibiyar al'adarsu ta wata, domin gane lokacin da yin jima'i zai iya kawo juna biyu.

'Sirri'

Kamfanin Apple ya ce masu amfani da manhajar za su iya fayyace ko wane irin abun bayanan da za su sa a ciki, da kuma sirrance abin da za a gani, saboda haka akwai doka ta sirri.

"Mutane dayawa na bibiyar abubuwa da yawa da ke taimaka masu wurin samun haihuwa," in ji Ricky Bloomfield, wani likita da ke jami'ar Duke, daya daga cikin wadanda ke mu'amala da sabuwar manhajar ta hanyar gwaji da marasa lafiya da ke zuwa wurinsa.

Hakkin mallakar hoto PATRIK STOLLARZ AFP
Image caption Abin gwada ciwon sukari a wayar Apple

Ya kara da cewa "Zai yi tasiri sosai wurin samun ingantaccen sakamako game da duk wani bincike da masu neman haihuwa za su yi."

Megan King ta shekara tana amfani da wani makamantan manhajar a baya kafin sabuwar ta i0S9 ta fito, kuma ta ce ta yi na'am da sabon tsarin.

"Wannan zai taimaka wa mata wurin bibiyar al'adar su, da kuma karin ilimi wurin tsaftace al'aura," in ji King.