'Yan gudun hijira sun kai miliyan daya a Girka

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Galibin 'yan gudun hijirar 'yan Syria ne

Hukumar 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya (MDD) ta ce a halin yanzu yawan 'yan gudun hijirar da ke isa Girka a bana ya wuce rabin miliyan.

Galibin 'yan gudun hijirar na tserewa rikice-rikicen da ake yi a Syria da Iraki da Afghanistan ne.

Jami'an majalisar dinkin duniya sun ce masu isa tsibiran Lebos da Chios a Samos da ke Girka basu ragu ba duk da cewa hunturu yana kunno kai.

Yawan 'yan gudun hijirar kimanin dubu 35 da suka isa Girka ta teku cikin kwanaki hudu da suka gabata, ya karu a kan yawan wadanda suka shiga lokacin bazara.

Hukumar ta nanata kiranta na cewa a samar da cibiyoyin tarbar 'yan gudun hijira a Girka, tana mai gargadi cewa idan babu, su shirin mayar da su muhallansu wanda gwamnatocin tarayyar turai suka cimma a watan da ya gabata ba zai yi tasiri ba.