Gas: Nigeria da Ghana sun sasanta

Image caption Ana fama da matsalar karancin lantarki a Ghana

Kamfanin man fetur na Nigeria, NNPC ya ce ya warware takaddamar da ke tsakaninsa da gwamnatin Ghana kan batun bashin kudin iskar gas.

Nigeria na bin kasar Ghana dala miliyan 170 na kudin iskar gas, abin da ya sa kasar ta yi barazanar rage yawan gas din da take tura wa Ghanar idan ba ta biya bashin da ake bin ta ba.

Sanarwar NNPC, ta ce a yanzu an kulla yarjejeniya kan yadda Ghana za ta biya bashin.

An cimma yarjejeniyar ce bayyan wata tattaunawa tsakanin shugaban Ghana, John Dramani Mahama da shugaban NNPC, Ibe Kachukwu da kuma ministan makamashin Ghana, Kwabena Donkor.

Nigeria ce ke samar wa Ghana wani kaso na iskar gas da kasar ke bukata domin bunkasa samar da lantarki a Ghanar.

A 'yan kwanakin nan, Ghana na fama da matsalar karancin wutar lantarki abin da ya sa gwamnatin kasar ke fuskantar caccaka, musamman kasancewa zaben shugaban kasa na tafe a badi.