An yi wa Oscar Pistorius daurin talala

Image caption Dan tseren Afirka ta Kudu Oscar Pistorius

An sako dan tseren nan na kasar Afirka ta Kudu Oscar Pistorius daga gidan yari, shekara daya bayan an daure shi sakamakon samun sa da aka yi da laifin kashe buduruwarsa Reeva Steenkamp.

An sako Pistorius ne kwana daya kafin ranar da hukumomi a kasar suka sanar da cewa za a mayar da shi zaman daurin talala na sauran wa'adin da ya rage a daurin shekaru biyar da aka yanke masa.

Hukumomi a kasar sun saki dan tseren ne a wani tsari da za a ci gaba da sa mushi ido daga gidan sa.

Dama tun a lokacin da aka yanke wa Oscar Pistorius hukuncin, ta bayyana cewa dan tseren zai iya samun irin wannan sassauci a gaba.

Sai dai a wanncan lokaci, ba a bayyana wa jama'a sharuddan sassaucin ba, amma da dama sun san ba za a makala na'urar lantarki a jikin sa ba wadda zata rika bada bayani game shi.

Yanzu za a takaita zirga zirgar sa, sannan ba za a bari ya mallaki bindiga ba, kana kuma za a rika yi mushi gwajin kwakwalwa a kai a kai a gidan kawunsa inda zai ci gaba da zaman daurin talala.

Ana kuma sa rai, za a sa dan tseren ya yi wa jama'a aikin tiki na tsawon wani lokaci.