'Sace mutane ya zama ruwan dare a Bukkuyum'

Image caption Sarki Muhammadu Usman na Bukkuyum

Wasu mazauna masarautar Bukkuyum ta jahar Zamfara, sun ce matsalar sace mutane domin neman kudin fansa tana son zama ruwan dare a yankin nasu.

Wani da ya zanta da BBC daga yankin, ya ce ya san akalla mutane 15 da aka yi garkuwa da su a yankin a baya-bayan nan, kana aka sako su bayan an biya kudin fansa.

Alhaji Buba Dikko ya shaidawa BBC cewar "galibin wadanda ake sace wa dattawa ne kuma sai an biya makudan kudade kafin a sako su."

Sai dai 'yan-sanda a jihar sun ce sun daura damarar yaki da masu garkuwa da mutanen, inda tuni suka fara kama wasu.

A cikin watan Maris ne aka wasu 'yan bindiga suka sace Sarkin masarautar Bukkuyum Alhaji Muhammadu Usman kafin 'yan bindigar su sake shi bayan mako daya a wani daji da ke kan iyakar jihar ta Zamfara da kuma Kebbi.