Rikici ya barke a Congo

Hakkin mallakar hoto

Akalla mutane hudu aka kashe a babban birnin Brazzaville na kasar Congo, a lokacin wata zanga zangar da aka yi kan shirye shiryen da shugaban kasar yake na tsayawa takara a karo na uku.

An ce 'yan sanda sun yi harbi kan masu goyon bayan 'yan adawa a kewayen kudancin babban birnin, yayin da mutanen suka yi kokarin dannawa cikin tsakiyar birnin.

An kone ofisoshin 'yan sanda da kuma motoci, sannan mutane na tserewa daga yankin da kayayyakinsu.

Kakakin gwamnati dai ya musanta cewa akwai wanda ya mutu, sannan ya ce lamarin bai kai ya kawo ba.

An dai katse harkokin sadarwa na intanet da sakonnin waya, sannan an rufe hanyoyin da za a iya sauraron gidan redion Faransa.