Boko Haram: An hallaka sojoji biyu a Diffa

Image caption Wasu 'yan Boko Haram a Diffa

Jami'an tsaro a jamhuriyar Nijar sun tabbatar da mutuwar soji biyu sannan ukku kuma sun sami raunuka a wani harin kunar bakin wake a Diffa.

Ministan tsaron kasar, Mahamadou Karidjo, ne ya tabbatar da hakan inda ya ce sojojin sun rasa rayukansu ne yayin da 'yan Boko Haram suka tayar da bama-bamai.

An kai harin ne a kusa da wani gari da ke yankin Diffa.

Wasu mazauna garin na Diffa dai sun ce an shafe daren ranar Talata ana jin karar harbe-harbe tsakanin jami'an tsaro da 'yan kungiyar ta Boko Haram.

A yanzu haka dai yankin Diffa ma karkashin dokar ta-baci a wani mataki na hukumomi domin su kawar da 'yan Boko Haram.

'Yan gudun hijira kimanin 150,000 daga Najeriya ne ke zaune a yankin domin tserewa hare-haren da Boko Haram ke kai musu.