Za a ci gaba da tantance ministocin Nigeria

Hakkin mallakar hoto national assembly
Image caption Majalisar dokoki ta tarayyar Najeriya

A ranar Alhamis ne majalisar dattawan Najeriya za ta ci gaba da tantance sunayen ministocin da shugaban kasar ya gabatar mata.

Majalisar ta dage zamanta na ranar Talata ba tare da ta sanar da dalilin yin hakan ba.

A bangare guda kuma, kwamitin da'a na majalisar dattawan ya ce ya kammala sauraron dukkanin korafe-korafen da aka gabatar wa Majalisar, domin neman ka da Majalisar ta tantance wasu da ake korafi a kan nada su ministocin kasar.

Mataimakin shugaban kwamitin da'a na Majalisar, Sanata Bala Ibn Na'Allah, ya ce majalisar ba ta shiga cikin sha'anin da ke gaban kotu, saboda haka za ta tantance tsohon gwamnan Ribas Rotimi Amaechi.