Aisha Buhari ta koka kan matsalolin 'yan gudun hijira

Image caption Dubban kananan yara ne ke fama da tamowa a sansanonin 'yan gudun hijira.

Matar shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta yi kira ga gwamnonin jihohin da ke fama da hare-haren 'yan Boko Haram da su dauki matakin gaggawa na magance matsalar mummunar yunwa a sansanonin 'yan gudun hijira.

Aisha Buhari -- wacce ta bayyana hakan a cikin sanarwar da mai ba ta shawara kan kan watsa labarai ya fitar -- ta ce kananan yara da mata da ke sansanonin 'yan gudun hijirar suna cikin mawuyacin hali.

Ta kara da cewa ko da a lokacin da ake cikin kwanciyar hankali kananan yara na bukatar kulawa ta musamman, tana mai cewa ya zama wajibi gwamnatocin jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa su dauki matakin gaggawa na ceto yaran daga mummunan halin da suke ciki.

Miliyoyin mutane ne suka tsere daga gidajensu sakamakon hare-haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai musu.